19th Ave New York, NY 95822, USA

RIGA-KAFIN CUTAR COVID-19: MATAN SAKKWATO SUN KARAYA SA KAMAKON ABUBAUWAN DA SU KA GANI A GWAJIN RIGA-KAFIN CUTAR SANKARAU A KAN

By Ayodeji Adegboyega| September 28, 2021

An bayYa na shi a matsayin “haramtaccen gwajin magani da ba a yi wa rajista ba,” a “bayYa nai dai kamar cin zarafi ne a sa kamakon karancin sani wasu,” da kuma “keta dokokin Najeriya da na ƙasa da ƙasa,” gwajin magani riga-kafin Trovan a shekara ta 1996 da wani kamfanin harhada magunguna mai su na Pfizer Inc. ya maida wasu yaran Najeriya a tsohon garin Kano kamar matsayin za karun gwajin dafi.

Sa kamakon irin mummunan sa kamakon da a ka samu wanda ya haifar da ta kaddama tsawon shekaru ma su yawa da kuma irin tashin hankali da kai komon shari’a da a ka tabka a tsa kanin kamfanin magunguna na Amurka da Najeriya. Akwai zarge-zarge da su ka wa kana a tsa kanin ” drama ‘persona’ amma wadanda abun ya shafa sun riga sun shuɗe.

A yau, shekaru 25 bayan mummunan abun da a ka gani a wannan lamari, har yanzu batun bai ɓace ba cikin tunanin tala kawan Najeriya, kuma da alama wannan lamari na cigaba da zama abunda ka iya kawo cikas hatta ga duk wani ƙoƙari na gaske don magance wasu matsalolin kiwon lafiya.

A Sakkwato, jihar da ke Arewa-maso-Yamma kamar Kano, abun fargaba  a nan shi ne sabbin wadanda za a yi wannan riga-kafi akwai yiwuwar su fuskanci matsaloli, kamar dai yadda wasu mutane da a ka zanta da su su ka fadi, cewar ba su saki jiki dan karbar ainihin riga-kafin da a ke bukata ba.

Wata mata mai su na Hauwa Mohammed, mai juna biyun ɗanta na huɗu, na ɗaya daga cikin matan da ke a ɗakin awon ma su juna biyu na ɗakin shan magani dake unguwar Mabera. 

Wasu sashin mata ma su juna biyu a wurin awon ciki a ɗakin shan magani dake Mabera Da ambaton ‘allurar riga-kafin cutar coronavirus’ daga wannan mai ba da rahoto, Malama Hauwa Mohammed ta fara nuna tashi hankalinta tare da nuna damuwarta, ta na nanata batutuwan da su ka danganci amana da aminci. Ta na ɗaga muryar fiye da sauran matan da ke ɗakin jira.

Da ta ke magana cikin nutsuwa a harshen Hausa, wanda shi ne asalin yaren ta, ta kalli wannan mai aika rahoto cikin shakku, wataƙila ta na tunanin ɗan jaridar ya na wurin don yin ma su allurar riga-kafin ne.

Malama Hauwa Mohammed ta ce “ba za ta amince da duk wani abun da ke zuwa daga ƙasashen yammanci duniya ba,” yayin da ta ba da labarin abun da ta bayYa na a matsayin “kisan gilla ga yara marasa laifi a Kano kan cutar sankarau da Pfizer ya yi.”

Ta ce; “Babu wani mai hankali da zai amince da wannan allurar; ko yaushe abunda za su aiko mana shi ne muggan lalattun magunguna saboda sun san mu na da yawa, domin haka su ke son shafe mu. Sun kashe mutane da yawa a Kano a waccan shekarar.

“Ee, mun yarda cewa akwai coronavirus, amma ba zan taɓa ɗaukar abun da ke zuwa daga turawa ba a matsayin mafita. Gara na yi amfani da ganye na maganin gargajiya. ”

Hakanan, a Gagi, wani ƙauye a gundumar Sakkwato ta kudu, da yawa daga cikin matan da wakilin ya zanta da su ba sa son rungumar allurar riga-kafin.

Zulihat Abdullahi ita ce shugabar mata a cikin garin, wacce, duk da haka, ta nuna damuwar ta cewa cutar ta kutsa cikin al’ummomin jihar Sakkwato, amma ta dage cewa ba za ta karbi allurar riga-kafin ba.

“Mun yi imanin cewa akwai kwayar cutar kuma mutanen da su ka kamu da cutar sun warke da maganin gargajiya. An kuma binne waɗanda suka mutu. Amma ina tabbatar mu ku cewa maganin gargajiyar mu, wanda a ke samu daga saiwoyi, su na da matukar tasiri wajen warkar da ma su cutar, ”in ji Malama Zulihat Abbdullahi.

Sai dai, duk da haka, ta yi gargadin cewa “idan mutane ba su yi imani da maganin ba, ba zai yi musu aiki ba,” ta kara da cewa “an yi maganin daga ganyayyaki kuma su na sa mutane samun sauƙi ba tare da wata matsala sosai ba.”

Da ta ke magana game da allurar riga-kafin COVID-19, shugabar matan ta ce tuni sun ruɗe da rahotannin mutane da yawa waɗanda a ka ce sun gamu da matsaloli bayan karbar allurar.

Da a ka tambaye ta ko sun yi kokarin tabbatar da sahihancin rahotannin, Malama Zullihat Abdullahi ta ce abunda su ka ji kuma su ka gani kan riga-kafin cutar sankarau a jihar Kano, isasshiyar shaida ce da ya kamata a amince wajen gaskata jita-jitar.

Ta ce; “Yar uwa ta daga Damboa ta kai ni cibiyar riga-kafin COVID-19 domin a yi min allurar. Kawai sai na ce ma ta na ji an yi wa mace allurar riga-kafin sannan ta suma.

“Mun jin labarin mutane su na biyan kuɗi har N40,000 don yin allurar amma ga cibiyar da ta kai ni, kyauta ce. Gara na yi amfani da kuɗin don kafa kasuwanci fiye da biyan kuɗi don samun allurar riga-kafi. ”

Ta ce ta ki karbar allurar riga-kafi duk da rokon da‘yar uwarta ta yi.

A yayin da take magana, Hauwa’u Umar, wata matashiyar uwa, ta lura cewa ta na sane da cewa allurar ta na da amfani amma ta dage cewa ba za ta karba ba.

Ta ce; “Na yi imanin akwai cutar COVID-19 kuma ina cikin mutanen da a ka shirya don wayar da kan mutane game da ita. Amma ba na son allurar saboda ban san yadda jiki na zai karbi abun ba. Ya na iya zama da amfani amma ba na so. ”

Ta ce cutar ta kara talauci a tsa kanin su, ta na mai cewa an rufe harkokin kasuwanci kuma yara sun kasa zuwa ma karanta na dogon lokaci.

Ta kara da cewa, “Mutane da yawa ba sa son a yi musu allurar riga-kafi saboda wasu na da ra’ayin cewa allurar ta na hana mutum haihuwa,” ta kuma kara da cewa; “Wasu na cewa idan a ka yi mu ku allurar za ku mutu amma ban san yadda gaskiyar ta ke ba amma ba na so a yi min allurar.”

Inno Ahmadu, kamar sauran mutane, ta yi imanin akwai cutar amma ba a yi mata allurar riga-kafi ba. Amma dalilin ta ya sha bambam.

Ta yarda cewa ta ji labarai marasa tushe da yawa game da allurar amma ta ce ba baYa nan karya ne ba ne dalilin da ya sa har yanzu ba a yi ma ta allurar riga-kafin ba.

“Saboda tsoron da na ke da shi na allurar ne kawai,” in ji ta.

Malama Inno Ahmadu ta ce ba ta iya zuwa  aikin hajji a Saudiyya a shekarar 2020 ba saboda cutar, kuma ta fahimci tsananin bala’in ta.

Ita, duk da haka, ta ce da an canza allurar riga-kafin zuwa kwayar magani, wataƙila da ta karba.

Kamar Mata, Mazan Ma Haka Su Ke

Segun Ilori Masani ne ta fuskar harhada magunguna da ke aiki da wata kungiya mai zaman kan ta da ke kula da saye da siyar da kayayyaki a jihar Sakkwato. Amma kwarewar sa ta likitanci ba ta hana shi jin tsoron allurar riga-kafin coronavirus.

Haka kuma ta wata fuska, bayan zurfafa tunani da jinkiri, ya karbi allurar riga-kafin ta farko, ‘yan kwanaki bayan da Najeriya ta ƙaddamar da shirin ta na riga-kafin cutar.

Sai dai kuma bayan ya yi riga-kafin, sai ya zama abun zargi tsa kanin abokan aikin sa. An sanya ma sa ido kan canjin ra’ayi, kamar yadda ya gayawa wannan mai ba da rahoto.

Ya ce; “Abokan aiki na a kullum su kan shiga ofis ɗi na don su duba ko ina lafiya. Wasu ma sun tsokane ni da wasu bayanai marasa kyau da su ka ji game da allurar.

“Sun ce sun yi tsammanin zan fara magana da harshe a murde, na yi tafiya da jan ƙafa ko kuma na ma rikiɗe daga mutum zuwa wani abun daban, kamar yadda su ka gani a cikin abubuwan da ke yawo daban-daban a kafafen sada zumunta. Amma duk sun ji kunya don hakan ba ta faru ba ”

Makonni bayan sanya ido a kan Ya nayin lafiyar Mista Ilori bayan da karbi allurar riga-kafin, abokan aikin sa biyu sun je yin allurar riga-kafin. Amma a cewar sa, wasu sun dage cewa ba za su karbi allurar ba “saboda tsoron abun da ba a sani ba.”

Allurar Riga-kafi a Najeriya

An kawo allurar riga-kafin a Najeriya a cikin watan Maris, shekara guda bayan an samu rahoton bullar cutar a ƙasar daga Legas, cibiyar kasuwancin ƙasar.

Kasar ta karɓi allurai miliyan 3.94 na allurar kamfanin Oxford-AstraZeneca ta hanyar cibiyar COVAX a farkon watan Maris, kuma ta fara yin allurar riga-kafin ga ‘yan ƙasa da su ka kawo kan su.

“Dangane da alƙawarin da mu ka yi, Babban Kwamitin Shugaban Kasa a Kan Covi-19 na ba da fifiko ga ma’aikatan kiwon lafiya da su ke sahun gaba a rukunin farko da za a mu su allurar riga-kafin ,” in ji shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan COVID-19, Boss Mustapha, a lokacin kaddamar shirin riga-kafin na ƙasa a babban asibitin kasa, da ke Abuja.

Likita Cyprian Ngong da ke a asibitin ya zama mutum na farko da ya fara karbar allurar riga-kafin a Najeriya.

Zuwa yanzu, jimlar ‘yan Najeriya 1,964,095 ne su ka cancanci yin allurar riga-kafin ta farko.

Dangane da bayanai daga Hukumar Kula da Kiwon Lafiya Matakin Farko (NPHCDA), hukumar da ke tsakiyar aiwatar da shirin allurar riga-kafin a Najeriya, ya zuwa ranar 28 ga Yuni, 2021, an gudanar da allurar riga-kafin 3,397,472.

Wannan ya nuna cewa nasarar da a ka samu ta yi kasa sosai, bisa ga manufar gwamnatin Najeriya ta son yi wa kimanin mutane miliyan 109 riga-kafin cutar COVID-19 a cikin shekaru biyu.

Yawancin ‘yan Najeriya sun yi niyyar gujewa allurar riga-kafin. A na iya danganta hakan ga jita-jita da makirce-makirce waɗanda suka dabaibaye allurar tun kafin ta iso Najeriya. An yi ta tsegunta kalamai marasa tushe da yawa da ke ikirarin nuna yadda mutane daban-daban su ke ji bayan karbar allurar, daga motsewar kashi da fita daga hankali, tawayar kafafu da tafiya, zuwa sarkafewar magana.

Bayan rahotanni na mutuwa da daskarewar jini a cikin mutanen da suka karɓi maganin AstraZeneca a Turai, an da katar dariga-kafin na ɗan lokaci. An yada labarin kan allurar riga-kafin da cewa ta na haifar da mutuwa a shafukan sada zumunta.

Ko bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar cewa a cigaba da allurar riga-kafin saboda fa’idarta ta fi haɗarin ta, wasu sun ƙaddara ba za su taɓa yin allurar ba.

Jin Ra’ayi

Dangane da binciken jin ra’ayi da dandalin sada zumunta na Twitter ya gudanar don sanin dalilin da ya sa mutane su ke bijirewa yin allurar, kashi 32 cikin dari na mutane 964 da suka kada kuri’a a cikin sa’oi 24 sun ce ba su amince da allurar ba.

Kashi 28 cikin dari sun ce akwai abubuwa da yawa da har yanzu ba a san su ba game da allurar, kashi 23 cikin dari su na tsoron illolin da ka iya biyo baya yayin da kashi 17 ne kawai ke son yin allurar amma ba su da lokacin zuwa.