19th Ave New York, NY 95822, USA

KUSKUREN ‘YAN NAJERIYA MA SU WA’AZI, CHRIS OKOTIE DA DAVID OYEDEPO, DANGANE DA ABUBUWAN DA KA IYA BIJIROWA BAYAN ALLURAR RIGA-KAFIN COVID-19

By Bukola Ayeni| September 28, 2021

Wani mawaki da ya juya zama mai wa’azi, Reverend Chris Okotie, ya cusa wa ‘yan Najeriya gurguwar fahimta a watan Yulin da ya gabata kan illar cutar COVID-19, in da yake cewa wadanda su ka karbi allurar riga-kafi za su zama ma su siffofin ma su shan jinin.

A cikin hirar bidiyo da a ka buga a ranar 12 ga watan Yuli na shekara ta 2020 a kan YouTube wanda sama da mutane dubu dari uku da saba’in da biyar suka kalla, Okotie ya bayyana allurar riga-kafin COVID-19 a matsayin shaidanci. Okotie, tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya yi ikirarin na karya ne da maganganu da dama tun farkon barkewar cutar COVID-19 a 2020.

Ya ce “abun da Bill Gates ke yi a karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya shi ne tabbatar da cewa kun karbi Abunci, da a ka jirkita ƙwayar halitta gadonsu watau (Genetically Modified Organisms) a Turance. Lokacin da ku ka ci wannan abuncin da a ka Sauya wa Halittu kuma ku ka karbi allurar riga-kafin COVID-19, kun shiga ciki ayarin Shaiɗan, Lucifer. Kuma daga wannan ne sai a wuce shan jini.

Yanzu, tunda ba jinin Yesu ba ne abunda mu ke magana a kai, ko abunda zai bayar, zai nemi ku nemi ku sha jini a wani wuri na daban. In da za ku iya samun jini Ya na cikin wani ɗan Adam. Don haka ɗaya daga cikin abubuwan da allurar za ta sa ku yi shi ne ku zama mutane ma su shan jini, wanda ke buƙatar shan jini don su rayu.

Amma mu, a matsayin mu na Kiristoci, ba mu shan jini, giyar bammi kawai mu ke sha; wanda ta ke karin jini kuma hakan Ya na ingata ma na ruhi. Amma mu’amalar su za ta buƙaci ku sha jini a kai -a kai don ku zama halittu ma su son ta’amali da jini don wadatar kan ku”

A watan Ogusta na shekara ta 2020 ta hanyar kafar sada zumunta ta WhatsApp, ya umarci mambobinsa da kar su sanya takunkumin rufe baki da hanci, Ya na mai jaddada cewa: “lokacin da mutum ya ke tsaye a gaban Allah a coci sanye da takunkumi ko abun rufe baki, Ya na nuna cewa ya yi inkari da mu’ujizar giciyewar da ka yi wa Almasi’u.” A cewar sa, sanya abun rufe baki Ya na nuna ‘inkari da iri abun da aikin Kristi ya kawo wa ‘yan Adam.’ Wannan bayani da a ka watsa shi ta hanyar manhajar  WhatsApp, ya zama babban labari a jaridu da dama. Koyarwar tasa ta zo kafin samun allurar riga-kafin COVID-19 a Najeriya.

A’a Sam, Riga-Kafin Covid-19 Bai Mayar Da Mutum Mai Shan Jinin Yan Adam

Dr Joe Abah, tsohon Darakta-Janar na Bureau of Public Service Reforms.A shafin sa na Twitter @DrJoeAbah ya ba da sanarwa a ranar 4 ga watan Yuni, na shekara ta 2021, cewa ya karbi allurar riga-kafin AstraZeneca COVID-19 ta biyu amma bai zama birin ba, don nunawa mabiyan sa cewa, ma su baza labaru marasa tushe game da allurar ba gaskiya su ke faɗa ba kamar yadda za ku gani a wannan hotu a kasa.

“Na karbi allurar riga-kafin AstraZeneca COVID-19 ta biyu a jiya. Ba wani abun damuwa da na ji ko kaɗan. Ban zama birin ba. Na ma goga mayen karfe a kafadar hannu na, ba wani abun na’ura da a ka dasa min. Don haka ku hanzarta ku je ku karbi  ta ku allurar riga-kafin in har ba ku yi hakan ba. Ina takaicin rashin gani ina musabiha da rungumar mutane” – a rubutun Dr. Joe Abah
“Na karbi allurar riga-kafin AstraZeneca COVID-19 ta biyu a jiya. Ba wani abun damuwa da na ji ko kaɗan. Ban zama birin ba. Na ma goga mayen karfe a kafadar hannu na, ba wani abun na’ura da a ka dasa min. Don haka ku hanzarta ku je ku karbi ta ku allurar riga-kafin in har ba ku yi hakan ba. Ina takaicin rashin gani ina musabiha da rungumar mutane” – a rubutun Dr. Joe Abah

“Mutane da yawa sun karbi allurar riga-kafin COVID-19, - sama da mutane miliyan 150 a fadin duniya da kusan milyam daya a Najeriya su ka karbi allurar riga-kafin. Allurar riga-kafin ba ta hada su da tsarin sadarwa na 5G ba. Ba ta dasa mu su wata na’ura a jikin su ba. Na karbi allurar riga-kafin, haka ma iyaye na. Ba mu zama fatalwa ma su shan jini ba #muamincedaallurar riga-kafinCOVID-19” a cewar Henry
“Mutane da yawa sun karbi allurar riga-kafin COVID-19, – sama da mutane miliyan 150 a fadin duniya da kusan milyam daya a Najeriya su ka karbi allurar riga-kafin. Allurar riga-kafin ba ta hada su da tsarin sadarwa na 5G ba. Ba ta dasa mu su wata na’ura a jikin su ba. Na karbi allurar riga-kafin, haka ma iyaye na. Ba mu zama fatalwa ma su shan jini ba #muamincedaallurar riga-kafinCOVID-19” a cewar Henry

Ƙarin Ma Su Wa’azi Sun Yaɗa Makamantan Wadannan Rikitattun Bayanai Hanyar Amfani ‘Ruhaniya’ Game Da Allurar Riga-Kafin Covid-19

Bishop David Oyedepo, wanda ke jagorantar Majami’ar Living Faith Church Worldwide, yayin da ya ke gabatar da wa’azi a hidimar bikin cika shekaru 40 da cocin ya yi, ya bi sahun ma su yaɗa farfagandar maƙarƙashiyar hana sanin gaskiya game da cutar COVID-19 a Najeriya, ya ce “bari in yi mu ku gargadi game da wannan mummunan abu (allurar riga-kafin COVID-19) da ta bazu ko’ina cikin ƙasar nan saboda ba a gwada shi da kyau ba. Wani dattijon wannan cocin, wanda ke aiki tare da Hukumar kula da Lafiya ta Duniya, ya tabbatar min da hakan, Ya na gode min a koda yaushe ina faɗin gaskiya game da ingancin allurar riga-kafi COVID-19. Babu wanda ke da ikon tilasta mu ku allurar riga-kafi, kuma babu wanda zai iya dakatar da aikin ku saboda kun ƙi karbar allurar, Allah ne zai bayyana mu ku abun da na ke nufi.

Su na son ‘yan Afurka su mutu. Na ji su na fadin haka. Lokacin da su ka ga ba mu mutu ba kamar yadda su ka tsara, sai su ka fito da wannan shirin allurar riga-kafin. Ya kamata ku ji abun da su ke ikirari da tutiya a cikin shirin su kan cewa kasashen dake cikin nahiyar Afurka zasu rasa filayen da zasu binne gawawwaki. Amma, a yau, sai ga a kasin haka ne ke faruwa. Afurka ita ce ke da mafi karancin asarar rayuka a tsakanin sauran nahiyoyin duniya.”

Kafin a samar da allurar riga-kafin, Bishop din ya soki gwamnati da rufe majami’u domin dakile cutar mai saurin kisa, Ya na mai cewa “rudin shaidan na shafar mutane a matakai daban-daban, su na kai hari kan cocin saboda cigaba da cocin ke samu shi ne ciwon kai mafi tasiri ga shaidan. Amma ƙofofin jahannama ba za su yi nasara a kan ta ba. Shaiɗan da dukkan wakilan sa za su girbi abun da su ke yi. Ban san bayanan da ke asibitin ba da abun da a ke rubutawa wajen warkarwa amma mu a cocin Allah ne ke buda ma na hanyar waraka. Kuma yanzu asibitoci, in da mutane ke mutuwa kowace rana, a buɗe su ke, amma an rufe coci saboda zaluncin shaidan ba shi da magani.”

Hakanan, babban fasto na LoveWorld Incorporated, dake da kimanin mabiya miliyan 13 a duk duniya (wanda kuma a ka sani da su nan Christ Embassy), a Legas, Najeriya, Chris Oyakhilome, ya tabbatar da cewa ikirarin kan cutar karya ne tun farkon barkewar cutar a kasar. A cikin wa’azin da a ka watsa a kan manhajar YouTube tare da mutane sama da 12,000 su ka kalla, ya yi iƙirarin cewa ƙaddamar da fasahar 5G ita ce ke da alhakin COVID-19. Ya kuma yi zargin cewa za a yi amfani da allurar riga-kafin COVID-19 a matsayin kafa don gabatar da “sabon tsarin duniya” wanda Dujal ke jagoranta. An goge wannan bidiyon, wanda a ka watsa a ranar 8 ga watan Afrilu, na shekara ta 2020 a dandalin YouTube.

Hanyar sadarwa 5G ita ce fasahar sadarwa mara waya da a ka ƙirƙira a jerin sahu na biyar na fasahar sadarwar salula.

Burtaniya Ta Sa Wa Fasto Chris Oyakhilome Takunkumi Bisa Da’awar Karya Game Da Covid-19

Ofishin Sadarwa na OFCOM, mai kula da kafafen watsa labaru na Burtaniya, ya sa takunkumi da kuma hana LoveWorld Television Network, tashar talabijin da Oyakhilome ya kafa a watan Mayu 2020 watsa shirye-shirye, don laifin yaɗa “maganganun karya game da cutar COVID-19. Takunkumin Ya na da alaƙa da yada bayanai na makirci wajen jingina hanyar sadarwa ta 5G wanda Gidan Talabijin na LoveWorld ta watsa shi ta tauraron dan Adam ga duk duniya.

Ikirarrin na ƙarya na cewar allurar riga-kafin ta na da alaƙa da layin sadarwa ta 5G makirci ne wadda ba wata hujja ta gaskiya da za’a dogara da ita. Lallai da yawa daga cikin ƙasashen da abun ya fi kamari ba su da hanyar sadarwa ta 5G, kuma an karyata ra’ayin cewa akwai nasaba tsakanin dogan karfen sadarwa na 5G da COVID-19 sosai, cikin wadanda suka karyata haka har da Dr Simon Clarke, Farfesa a ilimin ƙwayoyin cuta na ginin halittar Dan Adam in da ya tabbatar da makircin dangata sadarwar 5G da bazuwar cutar da cewar “zance ne marar tushe da kan gado.” Kamar yadda BBC ta ruwaito wannan tsokaci..

Shugabannin Addinai Da Annoba: Bangarori Biyu Da Su Ka Yi Hannun Riga

Addini da annoba koda yaushe su na tafiya hannun riga, bullar annobar cututtukan da suka gabata sun tabbatar da gaskiya haka.

Wata kasida mai taken “’17, ’18, ’19: addini da kimiyya a cikin annoba uku, 1817, 1918, da 2019” wadda Howard Philips ya rubuta, wadda kuma a ka buga a ranar 6 ga watan Nuwamba na shekara ta 2020 a Maɗaba’ar Jami’ar Cambridge, ta ba da bayani mai zurfi kan tarihin annoba daga mahangar addini. Wannan tsokaci Ya na magana game da cututtukan kwalara na farko da na biyu na shekara ta 1817 zuwa ta 1830 da cutar sankara ta Spain ta 1918 zuwa 1919, da COVID-19 dangane da martanin addini.

Cutar kwalara ta 1817 ita ma, ma su wa’azi na wancan lokacin sun yi mata mummunar fassara. A cikin labarin, Philip ya ce “Duka Ikklesiyar Orthodox ta Rasha da Cocin Roman Katolika sun fassara cutar kwalara a matsayin kayan aikin azabtar da allahnta a ɗabi’ar ɗan Adam. An buƙaci addu’o’i Dan Adam da tuba da gaggawa don an yi wa Allah laifi, in ji wani Malamin addini na Katolika a Ingila, yayin da bishop na Faransa su ma sun yi magana game da matsalar a matsayin waiwayowar da Allah ya yi saboda ‘da zunuban mu sa shi yi fushi da mu’ 

Bayan shekaru ɗari da ɗaya, an sami barkewar cutar mura a kasar Sifaniya a shekara ta 1918zuwa ta 1919, “yawancin addinai da ɗimbin ‘yan Afurka har yanzu su na ganin cewar fusata ubangijn su ne” ko allolin su ya jawo haka.

Cutar COVID-19 a yanzu ita ma da na ta kaso na shigar da sha’anin addini, don nuna wani abu a boye kamar yadda a ka gani a jawaban baya.

Tasirin Shugabannin Addinan Najeriya A Kan Mabiya

Shugabannin addini su na da tasiri mai ƙarfi a kan mutane yayin da su ke tsara ma su ra’ayin su da hangen nesa a zaman rayuwa. ‘Yan Najeriya su na son addini sosai. A wani bincike da BBC ta gudanar a shekarar 2004, Najeriya ce ƙasa mafi yawan mutane ma su son addini a duniya. Najeriya ta yi zarra da kusan kashi 100% na mutane da ke “son mutuwa saboda ubagijin su ko imanin su.” Binciken Cibiyar Bincike ta Pew mai taken “Makomar Addinan Duniya: Kan Tsinkayar irin Cigaban Yawan Jama’a, daga shekara ta 2010-2050” ya nuna cewa akwai Kiristoci 46.9%, Musulmai 51.1% da kuma kashi 2% na sauran nau’o’in addinai a Najeriya. A wannan bincike guda biyu, an nuna mutane ne ma su son addini sosai kuma su na ƙara tabbatar da cewa shugabannin addini su na da tasiri a kan mutane idan a ka kwatanta da shugabannin siyasa da na gargajiya.

‘Yan Najeriya da yawa za su saurare su kuma su gaskata kalmomin shugabannin addinan su fiye da shugabannin siyasa saboda rashin yarda tsakanin jama’a da shugabannin siyasa. An sani tsakanin mutane cewa duka shugabannin addini da na gargajiya a na girmama su sosai kuma mabiyan su ko al’ummomin su na girmama su sosai, saboda mutane su na riƙo da addini da daraja da kuma amincewa domin haɗin kai da shugabannin addini da mutane abu ne da ya ke a zahiri tun daga yankunan karkara a tsakani al’ummomi daban-daban.

Wani dalilin da ya sa shugabannin addini ke da iko da tasiri shi ne tun daga shekarar 2020, Najeriya na da ma su amfani da intanet miliyan 99.05. Shigar ta’amali da intanet ya kai kashi 46.6% na yawan mutane a shekarar 2020. Yawan mutanen Najeriya kusan miliyan 200 ne, wanda ke nufin kusan ‘yan Najeriya miliyan 100 ba su da damar shiga Yanar gizo tukunna, don samo ko tabbatar da bayanai da kan su. Wannan kuwa ya haɗa da dukkanin ba’arin shekaru. Wannan Ya na ƙara tabbatar da cewa shugabannin addini su na da mahimmanci a cikin yada bayanai. Labari mai dadin ji shi ne cewa a na hasashen cewa amfani da yanar gizo na Najeriya zai karu da kashi 63% a shekara ta 2025, mutane na iya samo ko tabbatar da bayanai da kan su.

A bayyane ya ke cewa kungiyoyi ma su zaman kan su da na gwamnati sun fahimci iko da tasirin da shugabannin addini ke da shi a kan mutane kuma hakan ya bayyana ɗaya daga cikin dalilan da ke akwai da zai sa su yi tasiri ga halayen mutane kan yarda da allurar riga-kafi.

Majalisar Dinkin Duniya (Un) Da Hukumar Kula Da Lafiya Ta Duniya (WHO), Sun Shigo Da Shugabannin Addini Cikin Batutuwan Cutar COVID-19

Majalisar Dinkin Duniya da sauran wasu Hukumomin ta, bisa kokarin su na hanzarta dakile cutar COVID-19, sun bullo da Samfurin Tsarin tattara bayanai don shigo da ƙungiyoyi da mabiya addinai daban-daban da Shugabannin Addini a kan teburi guda  karkashin taken: Addini da Cutar COVID-19; Yin Abinda Ya dace.

Ita ma Hukumar kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi wani abu makamancin haka. A ranar 7 ga watan Afrilu na shekara ta 2020, ta ƙaddamar da wani Fasalin Tsara Manufar Addinai a kan cutar COVID-19 wanda a ka kira da suna: Tattaunawa da Shawarwari domin Shugabannin Addinai da al’ummomin da su ke mabiya addinai a cikin Yanayi na Da’irar cutar COVID-19. Manufar samar da wannan fasali ita ce a tsara yadda za a shigo da shugabannin addini a yaki da cutar sarkewar numfashi Watau COVID-19.

Majalisar Dinkin Duniya, da hukumar WHO da sauran hukumomi sun yi tanajin aiki tare da shugabannin addini wajen yaki da cutar, sai dai kuma wasu fitattu daga cikin malaman addini na sanya matsaloli a cikin kokarin hukumomi da gwamnati na yaki da wannan cuta. A maimakon hakan sai su rika bi su na yada karairayi da labarun makirce-makirce a kan cutar.

‘Ya Kamata Ma Su Wa’azi Su Daina Yada Labaran Karya Game Da Allurar COVID-19’

Farfesa Oyewale Tomori, tsohon shugaban Cibiyar Kimiyya ta Najeriya, sanannen masanin ilimin kwayar halitta ne da ke cikin Dan Adam kuma mabiyin addinin Kirista, ya ce ikirarin da ma su wa’azi ke yi cewa COVID-19 na iya canza mutane zuwa dabbobi ba su da tushe a cikin Littafi Mai-Tsarki. Ya ce, “Ya kamata su daina yada irin wannan jita-jita ta karya. Ya kamata su tuna abun da Littafi Mai -Tsarki ya faɗa game da ƙarya da maƙaryata a cikin John sura ta 8 aya ta 44 (‘Ku daga uba ku ke, Iblis, da kuma duk abun da ku ke so ku yi shi ne don faranta ma sa rai. Shi mai hallakarwa ne tun daga farko. Ba zai tsaya da gaskiya ba, domin babu guntun gaskiya a cikin sa. Lokacin da Maƙaryaci ya yi magana, Ya na yi ne daga Yanayin ƙaryar sa kuma ya cika duniya da ƙarya. Sako daga littafi mai tsarki na Injila) da inda maƙaryata zasu ƙare Aya ta 8 (“Amma ga matsorata da marasa ban gaskiya da abun ƙyama [waɗanda ba su da halaye da mutuncin mutuntaka da aikatawa ko yin haƙuri da lalata], su ma su kisan kai, da ma su sihiri [da kayan maye), da ma su bautar guma ka da ma su sihiri [waɗanda ke aikatawa da koyarwa addinan ƙarya], da duk maƙaryata [waɗanda da gangan su ke yaudara da karkatar da gaskiya], ɓangaren su zai kasance a cikin tafkin da ke cin wuta, wanda shi ne mutuwa ta biyu. ”kamar yadda littafi mai tsarki na Injila ya jaddada).

Ya yi kira ga Kiristocin Najeriya da su duba duk abun da su ka ji kafin su yi imani da shi, Ya na kawo wani nassi, 1 Yahaya 4 aya ta 1: “Kada ku gaskata kowane ruhu, amma gwada son ruhun idan na Allah ne, domin akwai annabawan ƙarya da yawa.”

Ma Su Wa’azi Da Kira Sun Yi Kuskure, Miliyoyin ‘Yan Najeriya Sun Karbi Allurar Riga-Kafi

Babu wani ɗan Najeriya da ya karɓi allurar riga-kafi COVID-19 da ya zama fatalwa, sabanin ikirarin ruhaniya mara tushe da Fasto Chris Okotie ya ɗaga. Ba tare da bin gargaɗin ƙarya ba, ‘yan Najeriya sun yi tururuwa zuwa cibiyoyin allurar riga-kafin COVID-19.

Ya zuwa ranar 27 ga watan Yuni, na shekara ta 2021 “‘Yan Najeriya 2,241,662 da su ka cancanta an yi mu su allurar riga-kafin farko yayin da 1,155,810 na’ yan Najeriya da a ka yi wa allurar farko su ka karbi kashi na biyu.” Waɗanda su ka karbi kashi na biyu su na wakiltar kasha 57.4% na jimlar wadanda suka karbi kashi na farko.

Najeriya ta na jiran jigilar kawo allurar riga-kafin a karo na biyu na kusan allurai miliyan 4 na COVID-19 a watan Ogusta kuma kasar ta na shirin cigaba da bayar da allurai na zagayen farko, wanda a ka dakatar don adana wadatattun magungunan zagaye na biyu.